Wani malami a babbar makaranta dake kano ya amsa laifin haike wa dalibarsa

Ali Shehu lakcara ne a makarantar School of Technology dake Kano, inda wata kotun majistire dake kano ta bada umarnin aci gaba da tsare shi a gidan yari.

Dabo FM ta samo rahoton da jaridar Daily Nigerian ta rawaito cewa malamin dan kimanin shekaru 36 a duniya an kama shi bisa zargin guda biyu na cin amana tare da kokarin aikata laifi wanda yayi dai dai da sadarar panal kod ta 95 da 98.

Alkalin kotun Muhammad Idris ya bada umarnin ci gaba da tsare shi tare da dage shari’ar zuwa ranar 15 ga oktoba domin yanke hukunci.

Tun da fari dai wanda ya shigar da karar mataikin sufuritanda na ‘yan sanda Badamasi Aliyu, ya gaya wa kotu cewa wanda ake zargin ya aikata laifin a ranar 14 ga ogusta ne a Kano.

Masu Alaƙa  Sojoji ne suka fatattaki ‘Yan Sandan da suka kama ni, suka sakeni na tsere - Dan Kidinafa

Ya kara da cewa an shigar da karar ne ta hukumar karbar ‘korafe-korafen jama’a tare da yaki da cin hanci.

Gawuna ya kara da cewa a wannan rana ne wanda ake zargin wanda lakcara ne a kwalejin fasaha dake Kano misalin karfe 11 na safe ya dauki dalibar sa wadda aka boye sunanta zuwa Ummi Plaza domin taya shi makin jarrabawa.

“A wannan yanayin ne wanda ake zargin ya kai mata hannu”

Daga baya dai ya amsa laifin sa.

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.