Labarai

Boko Haram ta afkawa mutanen Chibok, sun cinnawa gidaje wuta

Mayakan ta’addanci na Boko Haram sun afka karamar hukumar Chibok dake jihar Borno kamar yadda Jaridar TheCable ta rawaito.

Jaridar tace majiyarta ta cikin jami’an tsaro sun bayyana mata cewar dakarun sojin sun hada runduna domin fafatawa da mayakan.

Wani mazaunin garin ya bayyana cewar mayakan kungiyar sun shiga garin ne da misalin karfe 6 na yamma suna harbe-harbe tare da kona gidajen mutane.

“Yanzu da muke magana, mutane suna ta gudu domin tsira da rayukansu.

UA-131299779-2