Labarai

Gobarar Legas: Ganduje na cikin gwanonin da suka yi alkawarin bada tallafin miliyan 200

A wata ziyar jaje da gwamnoni 7 suka je yo jihar Legas bayan fashewar bututun man iska na Gas, gwamnan Kano, DR. Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana zasu hada tallafin 200m domin rage radadi gobarar da tayi asarar mutune da dama.

Majiyar DABO FM ta bakin mai bawa gwamna shawara na fannin yada labarai, Salihu Tanko Yakasai, ya bayyana cewa

” Mai Girma Gwamna Abdullahi Umar Ganduje OFR tare da takwarorin sa na kungiyar Gwamnonin Najeriya karkashin jagorancin gwamnan Ekiti, Kayode Fayemi da kuma gwamnan Edo, Obaseki sun kai ziyarar jaje jihar Lagos sakamakon fashewar bututun man fetir da yayi sanadiyar mutuwar sama da mutane goma sha bakwai da kuma asarar dukiya mai yawa.”

“Gwamnonin sun yi alkawarin hada tallafi na kudi Naira miliyan 200 domin taimakawa wadanda abun ya shafa”

A ranar 15 ga watan Maris din da muke ciki ne dai gobara sakamkon fashewar bututun mai ta afku wacce rahotanni suka bayyana anyi asarar rayukan, dukiyoyi, makarantu, gidaje da shagunan kasuwanci dayawa.

UA-131299779-2