Goron Juma’a: Bai dace fadin kalmar ‘RIP’ ga mamaci ba

Cikin wannan yanayi na zamantar da kowanne al’amari kama daga wanda ya dace da wadanda ba’a iya canzasu kamar na addini, fadin ‘RIP’ ya zama ruwan dare a bakin musulmai musamman masu kiran kansu da wayyayu.

Wasu daga cikin masu fadin ‘RIP’ suna masa kallon yana daukar ma’ana irinta addu’ar “Allah Ya jikai, Allah Ya gafarta.”

Wannan furcin baya cikin kyawawan addu’o’in da Annabin Muhammadu (Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya koya wa al’ummar Musulmi, hasalima al’ada ce da ko a addinin Kiristanci ba’a koya haka ba.

Masana addini sunce ‘RIP’ ba addu’a bace illa magana gama gari kamar kowacce kuma bata nuni da addu’ar nemawa mamaci gafaraa daga wajen Ubangiji.

Masu Alaƙa  Zagin Shuwagabanni da Malaman Addini tamkar zubar da jini ne - Dr Rijiyar Lemo

Musulunci addini ne cikakke, saboda haka malamai ke kira ga Musulmi su bi abinda addini ya zo dashi, a kuma kauracewa bin hanyar Nasara da makamantansu.

A matsayin musulmi, fadar;

  1. Allah ya gafarta musu
  2. Allah ya saka musu da gidan Aljannar Firdaws.
  3. Ya Allah Ka haskaka kabarinsu, ka gafartar kura-kurensu.

Da dai sauran wadanda basu sabawa dokar Allah ba.

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.