Labarai Nishadi

Darakta Hassan Giggs zai dauki nauyin yi wa wani matashi tiyatar ido

Darakta Hassan Giggs na masana’antar Kannywood ya dau alkawarin daukar nauyin aikin ido na wani matashi mai suna Sani Lawal dake fama da ciwon ido wanda ya tai ga makantarshi.

Daraktan ya bayyana ne haka ne bayan ziyartar matashin gidansu a garin Daura na jihar Katsina a arewacin Najeriya, inda ya ce ya cika cikin tausayi bisa irin yanayi da ya matashin.

DABO FM ta tattara cewar Darajra Giggs ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Najeriya ‘NAN’ cewar ya ga hoton matashin a shafin ‘Instagram’ ya kuma yanke shawarar taimaka masa.

Yace zai dauki nauyin aikin idon matashin a asibitin Ido na Makkah dake a jihar Kano.

“Ko nawa ne kudin zan biya masa. Na kuma shirya taimakonshi kuma zan zan kaishi ko ina a fadin duniya don neman lafiyar tashi.”

Ya kuma bayyana zuwa yanzu, za’a kai matashin asibitin Makkah dake Kano domin fara duba shi da shawarwari daga masana.

“Ranar Lahadi zai je Kano domin ayi gaggawar fara dubashi, kuma zan dauki nauyin wata dawainiya kama daga abinci, situra da duk abinda ake bukata.”

“Ina son ganin Lawal ya koma makaranta tinda yanzu ya kammala matakin firamare kuma yana son cigaba.”

“Muna son daukar nauyin karatun har zuwa ya gama Jami’a da ni da abokan sana’ata.”

Darakta Giggs ya baiwa iyalan matashi tsabar kudi na N40,000 domin fara rage wasu dawainiyarsu.

A nashi bangaren, mahafin matashin, Mallam Lawal Isah, ya bayyana godiyarshi ga Hassan Giggs tare da sauran abokanshi bisa son taimakawa dan nashi.

Sani Lawal ya fara idanunsa a shekarar da ta shude tare da cewar iyayenshi basu iya daukar nauyin nema masa lafiya ba bisa yanayin rashi.

Masu Alaka

Kotun ta bawa CP Wakili umarnin kama Hadiza Gabon

Dabo Online

KANNYWOOD: Amina Amal ta maka Hadiza Gabon Kotu bisa tuhumar cin zarafi

Dangalan Muhammad Aliyu

Shekaru biyar da rashin Dan Ibro: Waye ya maye gurbinshi?

Dabo Online

Dalilin da ya sa aka ji ni shiru – Mahmud Nagudu Tattausan Lafazi

Dabo Online

Yacce yan matan Kannywood suka shilla yawan shakatawa a manyan biranen duniya

Faiza

Gobara a KANNYWOOD: Adam A. Zango ya zazzagi Ali Nuhu

Dangalan Muhammad Aliyu
UA-131299779-2