Badaru Abubakar
Labarai

Gwamna Badaru ya kafa kwamitin aiwatar da fara biyan albashin N30,000

Gwamnatin Jihar Jigawa ta shirya tsaf domin fara biyan sabon mafi karancin al bashi wata maizuwa.

Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Muhammad Badaru Abubakar ne ya tabbatar da hakan, lokacin da yake jawabi ga kungiyar malaman Makaranta reshen Jihar Jigawa, a taron ranar malaman makaranta na duniya da akayi a birnin Dutse.( World Teachers Day)

A cewar sa, gwamnatin jihar ta kirkiri kwamitin na mutun shatara domin su tabbatar da anwaitar da sabon tsarin albashin.

Tun a baya dai in ba a manta ba, Gwamna Badaru ya yi ikirarin cewa shi ne Gwamnan da zai zamo na Biyu a biyan sabon albashin.

Tuni dai Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-rufa’i ya biya ma’aikatan jihar sabon albashin a watan da ya gabata.

Karin Labarai

Masu Alaka

Gwamna Badaru ya amince da gabatar da Sallar Idi a jihar Jigawa, ya gindaya sharuda

Dabo Online
UA-131299779-2