Labarai Sabon Labari

Gwamnatin Gabon ta tsayar da yunkurin juyin mulki, ta kama sojoji

Gwamnatin kasar Gabon tace ta samu tsayar da yinkurin da sojoji sukayi nayi mata juyin mulkin a safiyar Litinin.

An kama sojoji biyar dasuka jagoranci kwace gudanarwar babban gidan rediyon kasar kamar yadda kakakin gwamnatin Guy Betrand ya shaidawa Radio France International.

An kafa dokar hana fita a Libreville babban birnin kasar.

A safiyar Litinin ne sojojin suka bada sanarwar kwace jan ragamar mulkin kasar da shugaba Ali Bango yake jagoranta tin shekarar 2009.

Karin Labarai

UA-131299779-2