0
Sojojin sun bayyana sanarwar kwace mulkin bayan da suka kwace gudanarwar gidan radiyon kasar.
A safiyar Litinin din nan ne sojojin suka bayar da sanarwa a wata tashar talabijin a kasar yayin da sukayi ikirarin kwace mulkin ne saboda dawo da dimokradiyya a kasar dake yammacin Africa.
Sojojin sun kwace mulkin daga hannun gwamnatin da shugaba Ali Bango yake jagoranta mai rike da mulkin kasar tin shekarar 2009.
Mazauna babban birni kasar sun bada rahotan cewar; motocin sojoji su na ta kai-kawo a kan titunan garin na Libreville.
Shugaba Ali Bango yanzu haka yana kasar Morocco domin yin jinyar matsanancin ciwo tin wajan Oktobar shekarar da ta gabata.
