Home LabaraiAn maka muƙarraban gwamnatin tarayya da suka je jana’izar Abba Kyara a kotu

An maka muƙarraban gwamnatin tarayya da suka je jana’izar Abba Kyara a kotu

by Muhammad Isma’il Makama
0 comments

Kotu ta sanya ranar 30 ga Yuni domin fara sauraron karar da aka shigar kan wadanda suka halarci binne marigayi shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin Tarayya, Abba Kyari a ranar 18 ga Afrilu.

DABO FM ta tattara cewa cikin wadanda aka maka a kotun sun hada da sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha; ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika; ministan harkokin kasashen waje, Geoffrey Onyema, da wasu karin mutum 10.

Tinda fari dai lauyen dake kare hakkin bil’adama, Tope Akinyode ne ya shigar da karar a kotun majistire ta Wuse Zone 2, wanda Alkalin alkalan babban birnin tarayya ya nemi fayel din da ya shafi yan siyasa daga hannun alkalin dake sauraron karar, Alkali Zubairu Mohammad. Daga bisani Alkalin Alkalan ya boyefayel din ba tare da wani karin bayani ba.

A ranar Litinin ne Rijistaran kotun, Mr Yahaya ya bayyana mana cewa an kara bankado shari’ar wadda kotun Life Camp, Kado, Abuja zata saurara. Hakan ya biyo bayan yanda ba’abi dokokin kare kai daga annobar ba kamar yadda gwamnatin tarayya ta gindaya, wanda yan Najeriya da dama sun tsinci kansu a kurkuku biyo bayan karya dokokin da aka saka, musamman ma kan karya dokar kulle.

Sauran wanda aka maka sun hada da, mai taimakawa shugaban kasa kan yada labarai, Garba Shehu; mai bada shawara ta fannin tsaro, Babagana Moguno; da Ahmed Rufai; tare da ministar walwala da jin kai, Sadiya Farouq; sai kuma Amb Lawal Kazaure.

Ragowar sun sune da, Bashir Ahmad, Yusuf Sabiu aka Tunde, Musa Daura da Dr. Sani Aliyu. Kamar yadda ThePunch ta fitar.

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00