/

Mawakan ‘Hip-Hop’ 2 sun gina titi mai tsawon kilomita 2.5 a jiharsu ta Anambra

Karatun minti 1

Fitattun mawakan Najeriya, Kcee da dan uwanshi E-Money, suna gina titi da tsawonshi ya kai kilomita 2.5 a garinsu na Uli dake jihar Anambra.

Kcee fitaccen mawakin da yayi wakar Limpopo, wacce ta shahara s hekarun baya.

Daga cikin mawakan, Kcee ya bayyana yacce aka ci karfin aikin a shafinshi na Instagram, inda ya bayyana cewar nan ba da dadewa ba za’a kammala aikin titin.

“Domin soyayyar gari na na ULI, ana cigaba da yin aikin titi mai tsawon kilomita 2.5. Mutanenmu suna farinciki saboda ni da dan uwana.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog