Labarai

Taron N10,000: Ku hanzarta ku biya, zaku ji labari na da wani bai taba fada ba – Zahra Buhari

Cece-kuce ya barke tin dai bayan fitowar batun taron da diyar shugaba Muhammadu Buhari ta shirya wanda mahalarta taron zasu biya N10,000 a matsayin kudin shiga.

Zahra dai ta shirya taron ne domin baiwa mutane labarinta na musamman wanda tace zai taimakawa mahalartan wajen kauracewa cin zarafi ko barazanar shafukan yanar gizo-gizo.

Da take kara bayyana a shafinta na Instagram, Zahra tayi kira da mutane masu sha’awa da suyi sauri suyi rijista domin “An kayyade adadin maharta taron”, ta kuma alkaurantawa mutane jin sabon abu wanda wani bai taba fada ba.

“Kuyi sauri kuyi rijista domin samun gurbi, hakika babu kokwanto, zakuji abinda wani bai taba fada ba.”

”Labari na kashin kaina akan kaucewa barazanar yanar gizo-gizo.”

“Zan taimaka muku wajen ginin kwarin gwiwarku da zaku iya tsayawa tsayin daka a bainar jama’a.”

Duk da cewa Zahra ta bayyana cewa zata sanya kudin shigar na N10,000 a cikin asusun gidauniyar da take jagoranta na taimakon marasa karfi wanda har ta kai ga ta bude musu gida na musamman.

Sai dai hakan bai sa mutane su dena sukar ta ba bayan sun kira shirin ‘Taron karbe kudaden a hannun mutane.’

Karin Labarai

Masu Alaka

Zahra Buhari ta shirya taron bada shawarwari, mahalarta zasu biya kudin shiga na N10,000

Dabo Online
UA-131299779-2