Labarai

Sojoji sun fatattaki ‘yan Boko Haram yayin harin Damaturu

Rundunar Sojojin sashin Lafiya dole dake aiki a jihar Yobe, ta tabbatar da fatattakar yan Boko Haram da suka kai hari a garin Damaturu, babban birnin jihar.

Mai magana da yawun sashin Sojojin na jihar, Kaftin Njoka Irabor ne ya bayyana haka a daren ranar Lahadi.

“Yan Boko Haram sunyi yunkurin shiga garin Damaturu, sai dai jami’anmu sun fatattake su.”

Kaftin Irabor ya bayyana cewa sai zuwa gobe za’aji cikakken bayani.

A daren ranar Lahadi ne dai rahotanni daga garin Damaturu na jihar Yobe suka tabbatar da hari da kungiyar Boko Haram suka kai zuwa garin.

Mazauna garin sun bayyana yacce mayakan ta’addanci na Boko Haram sukayi tayin luguden wuta ana tsaka da gudanar da rayuwar yau da kullin.

UA-131299779-2