Matsalarmu a Yau Taskar Matasa

Taskar Matasa: Sai an cire son zuciya za’a iya magance matsalar Almajiranta – Zainab Naseer

RA’AYINA AKAN MAGANCE MATSALAR ALMAJIRANCI

Almajiranci ya zama al’adar arewacin Nigeria. saboda haka ni a ra’ayina batun a ce za a magance matsalar a lokaci daya bai taso ba. Saidai in kawai a kawo gyara a harkar domin kawar da ita zai yi wahala idan ma zai yiwu kenan. Sanin kowa ne cewa al’ummar mu basa yin wasa da duk wani abu da ya shafi addini, idan ma ka fiye maganar zaka kawar da almajiranci wasu zasu fara tunanin kai makiyin musulinci ne.

Ga dai wasu yan hanyoyi da nayi nazarin idan an bisu za a magance matsalar da take tattare da almajiranci.:

– Dole sai an gyara zuciya, wani marubuci yana cewa “tunaninka kamanninka” sai mun gyara zuciya da tunanin mu sannan zamu fuskancin magance wannan matsalar. A cire duk wani son zuciya a kalli almajiranci a matsayin wani abu da yake bukatar gyara daga gurin al’umma da duk wadanda abun ya shafa.

– Kawo tsare tsare a cikin yanayin turo su wadannan yara. Yakamata a ce iyayen kowane almajiri su rinka kawo kudin bukatun yau da kullum na kowane yaro idan zasu turo shi almajiranci. Kama daga cin sa, sha, sutura, kudin magani idan ba lafiya da sauran bukatun yau da kullin.

– Yazamana su alarammomin su daina karbar kowane yaro idan har iyayen sa basu bada kudin bukatun sa ba. Yin hakan zai magance matsalar barace barace da yaran sukeyi da kuma irin hadarurrukan da zasu fada idan suna yawace yawacen neman abun da zasu ci kuma ya kare su daga kamuwa da cututtuka.

– Koyar da sana’o’in dogaro ga kai gasu wadannan yara ya zamana ba wai iya karatun za a yi ba kawai, a ware wani lokaci da za a rinka koya musu Sana’a.

– Gwamnatoci da hukumomi su saka dokoki kuma a saka ido domin tabbatar da dokar cin zarafin yara wato (child right acts) kuma tare da daukar hukunci akan duk Wanda aka kama da cin zarafin almajirai.

Kungiyoyi masu zaman Kansu su rinka shiga cikin makarantun tsangayar nan domin ganin matsalolin su da kuma kirkiro da hanyoyin da zasu tallafa musu ta fannoni daban daban na rayuwa.

Kowa dai yana da rawar da zai taka daga iyaye, gwamnati har al’umma gabadaya.
‘Da dai na kowane,
Almajirai ma yaya ne.

Zainab Nasir Ahmad
2/4/2019

Masu Alaka

Matsalarmu A Yau: Bara ba Addini bace

Dangalan Muhammad Aliyu
UA-131299779-2