Matsalarmu a Yau

Matsalar Tsaro: Akwai buƙatar a tuna maka Baba, Daga Rabi’u Biyora

Wallahi Tallahi al’ummar Nigeria sun kaunaceka ne sakamakon sanin da sukayi maka na jarumin soja, wanda ko kadan baka wasa idan akayi abun dazai cutar da rayuwarsu.

Sanin gwagwarmayar da kayi lokacin kana gidan soja, da dagewarka wajen kare Najeriya da mutanen Najeriya, hakan ne yasa tun shekarar 2003 daka fara nuna sha’awar shiga siyasa al’umma kasar suke ta murna tare da adduar Allah yasa ka zama shugabansu, domin suna da yakini akan cewa bazaka taba zuba idanu idan ana zaluntarsu ba…..

Baba Buhari gaskiyar magana masoyanka suna cikin tashin hankali sakamakon irin munanan kalaman da’a yanzu ake iya furtawa akanka, ba tare da shakkar komai ba, wanda hakan yana faruwa ne sakamakon wasu lamura dake faruwa na tsaro da wasu mutanen ke ganin kamar kana sane kake zuba idanu ba tare da ka tsawatar da jami’an tsaro sun dauki matakin gaggawa ba.

Don Allah Buhari kayi abun daya kamata wajen daukan matakin dazai kawo karshen kashe kashe tare da sace mutanen da akeyi a Arewacin Nigeria.

Rabi’u Biyora

Karin Labarai

Masu Alaka

Arewa ta samu karuwar masu digiri na biyu sama 30 daga Jami’a daya a kasar Indiya

Dabo Online

Ko Abba zai zamo mafi alkhairi a Kano, Allah kada ka bashi nasara – Usman Liti

Dangalan Muhammad Aliyu

Sulhun shafaffu da mai a karamar hukumar Fagge

Dabo Online

‘Yan daba sun kai hari, gidan shugaban APC na jihar Kano

Dabo Online

Matasa sun kone motocin APC a Abuja

Dabo Online

Saurayi ya kashe kanshi bayan zargin fyade

Dabo Online
UA-131299779-2