Yadda ‘yan mata su ka ba wa hammata iska wajen siyan gwanjon Abaya

Karatun minti 1

Tin bayan zancen yayin shigar Abaya tsakanin ‘yan mata a wannan sallar, al’amarin su ka yi da janyo cece-kuce tsakanin al’umma a shafukan sada zumunta.

Ba iya shafukan sada zumunta ba, hatta malamai sun tofa albarkacin bakinsu har wa wadansu daga ciki su ka yi kakkausar nasiha a kan batu.

A wani bidiyo da DABO FM ta samu, ya nuna yadda wasu rikici ya kacame a wata kasuwa siyar a yayin siyan tasu Abayar da za su fi bikin Sallah da ita.

Abayar da ake siyarwa a wajen, a abaya ce ta gwanjo da aka fi kiranta da sunan ‘Gumama.’

Duk da DABO FM ba ta iya gane a ina abin ya faru ba, bidiyon ya tabbatar da faruwar al’amarin kuma dukkanin alamu sun nuna a Arewacin Najeriya ne.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog