Ra'ayoyi

Ranar yaki da cin hanci da rashawa ta duniya: Ta wacce hanya za’a yin magani a Najeriya?

A rana irin ta yau, majalissar dinkin duniya ta ware domin duba yanda cin hanci da rashawa yake a sassa daban na duniya da kuma irin illarsu.

Sanin kowa ne, a yau a Najeriya wannan lamari ya shiga wani mataki na sai dai kawai addu’a. Domin ba wani sashi ko bangare da za ka je ba ka samu rashawa ba.

Abubuwan ban mamakin shine, lamarin ya karade har bangarorin addini. Domin an taba bani labarin wani malami da ya bayar da cin hanci domin a nadashi limamin masallachin juma’a.

Wannan lamari ya kutsa ko ina, neman kwangila, aikin gwamnati, karin matsayi, sauyin wajen aiki, siyan shari’ah da su siyan sakamakon jarabawa. Auratayya ma ta fara ginuwa akan cin hanci. Don an sha ganin hakan sau da dama.

Idan kuwa har hakane, ba shakka mun shiga wata rayuwa sai dai ace innalillahi. Domin mun kwana da sanin hukuncin mai bayarwa da mai karba. Sai dai haakan ya zamar mana jiki ba mu damuwa ko kadan.

Akwai wani lokaci mun je asibiti na raka abokina, wajen 11am haka. Mutane jingim a layi. Bayan ya mika katin, ana fara kiran sunaye, sai naji an kirashi wajen na biyar. Bayan an dubashi mun futo, sai nake cewa ya haka aka kiraka da wuri? Sai yace ai wai kudi ya makala a jikin katin ya bawa mutumin mai kiran sunayen… Nayi mamaki.

Dole komai ya shiga wani hali a wannan zamani. Rashawa ta gama zama tushen farko wajen tabbatar da wasu lamura na rayuwarmu. Kuma idan har ba ayi da gaske ba, za mu jima cikin matsaloli.

Hassan Muhammad Ringim 🖊

UA-131299779-2