Labarai

Wani Kamfanin maganin kashe kwari ya dauki mutumin da Tusarshi take kashe sauro

Joe Rwamirana, mai shekaru 48 dake da zama a birnin Kampala na kasar Uganda, ya fara samun miliyoyin kudade bayan da kamfanunuwan maganin kwari suka gane ‘Tusarshi’ tana kashe Saura da wuri.

Zuwa yanzu, wasu daga cikin kamfanunuwan maganin Sauro a kasar suna biyan Joe domin yin nazari akan nau’in tusar da yakeyi tare da mayar da ita sinadarin hada maganin a Kamfanin.

Jaridar Talk ta tattaro cewa Tusar Joe tana kashe dukkanin wani kwaro da yake kusa da Joe zuwa tsawon mita 6.

Haka zalika ta tabbbatar da cewa Tusar tana kashe Kwaruka masu tashi wadanda basu fi girman Sauro ba.

Itama Jaridar Independent ta Najeriya ta shaida cewar; Tin lokacin da Joe yake karamin Yaro, ya kasance garkuwa ga mutanen gari musamman manyan kauyensu, wanda sukan kaishi gidajensu a lokacin da cutar cizon Sauro ta barke a kauyen.

Independent tace duk wanda yake kwana tare da Joe bai taba kamuwa da ciwon Malaria ba, haka ma shi kanshi bai san yay cizon Sauron ma yake ba.

DABO FM ta binciko matashi yana karin haske game da batun, inda ya bayyana;

“Ina cin irin abincin da kowa yake ci, amma babu wani Kwaro da yake iya hawa jiki na ko da kuwa mai tashi ne.”

Ina wanka kullin, kuma Tusa ta irinta kowa ce, sai dai tawa Tusar tana kashe kwari musamman Sauro.”

UA-131299779-2