Labarai

Ganduje ya nada Sarki Sunusi shugaba a Majalissar Sarakunan Kano da wa’adin shekara 2 kacal

Gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahii Umar Ganduje, ya nada Sarkin Kano, Muhammadu Sunusi II, a matsayin shugaban Majalissar Sarakuna da dattawan jihar Kano.

Hakan na zuwa ne bayan tsammani da al’umma sukayi akan yiwuwar nada Sarkin Bichi, Alhaji Aminu Ado Bayero a matsayin shugaban Majalissar.

Da yake bada sanarwar, Abba Anwar, mai magana da yawun gwamnan Kano, ya bayyana cewa gwamnan ya bawa Sarki Sunusi umarnin kiran taron Majalissar da gaggawa.

“Gwaman jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje, ya nada mai martaba Sarkin Kano bisa ikon da sashi na 4 (2) (g) da sashi na 5 (1) (2) na dokar Majalissar Masarautar Kano, a matsayin shugaban Majalissar.”

”Kai tsaye, dukkanin Sarakuna masu daraja ta daya na masarautu Bichi, Gaya, Karaye da Rano sun zama daga cikin wannan majalissar kamar yacce dokar ta tanada.”

“Duk dai bisa sashi na 4 (2), Majalissar ta kunshi Sakataren gwamnatin jiha, Kwamishinan kananan hukuma da shuwagabannin kananan hukumi 5 da Sarakunan suke, dukanninsu a matsayin mambobi.”

Abba Anwar ya kara da cewa; Majalissar ta kunshi masu nadin Sarki guda 10 (Guda 2 daga cikin Masarautu 5), tare da babban limamin kowacce Masarata.”

Sauran membobin sun hada da wakilcin ‘yan kasuwa daga yankunan kowacce masarauta, wanda gwamna zai nada su.

Tini dai gwamnan Kano, Dr Ganduje ya nada Alhaji Dalhat Al-Hamsad da Alhaji Auwalu Abdullahi Rano a matsayin wakilan ‘yan kasuwar.

Ya tabbatar da cewa; Bisa tsarin dokar, za’a rika chanza shugabancin Majalissar tsakanin Sarakuna 5 na Kano duk bayan shekaru 2 – Kowanne Sarki zai rike shugabancin na tsawon shekara 2 kacal.

“Majalissar zata fara aiki daga ranar 9 ga watan Disamba.”

“Gwamna ya umarci shugaban Majalissar, Sarkin Kano Muhammadu Sunusi II, ya hada taro da gaggawa domin rantsar da membobi da ‘yan Majalissar Masarautar cikin gaggawa.”

Karin Labarai

Masu Alaka

Hotuna: Ganduje ya kai ziyara filin da za’a kara rantsar dashi don shiga “Next Level”

Dabo Online

Galadiman Kano ya cika shekara biyar da rasuwa

Muhammad Isma’il Makama

Ganduje ya sake nada Ali Baba Agama Lafiya a matsayin mai bashi shawarar addinai

Dabo Online

Kwankwaso ya tura matasa neman Ilimi, Ganduje ya bude cibiyar koyar da gyaran mota

Dabo Online

Zaben Gwamnoni: Zan karɓi kayi idan na fadi zabe – Ganduje

Dangalan Muhammad Aliyu

Ganduje na shirin ayyana Sarkin Bichi a matsayin babban sarki a Kano

Muhammad Isma’il Makama
UA-131299779-2