(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

Ko gwamnati ta bude makarantu muna nan kan bakarmu ta cigaba da yajin aiki -ASUU

dakikun karantawa

Kungiyar malaman Jami’o’i reshen Jami’ar Ahmadu Bello Zaria ta jaddada cewar yajin aikin da take yi yanzu haka ba tana yin shi ba ne domin jindadi, sai domin ceto harkar Ilimi a Najeriya kuma makarantu su samu nagartaccen tsari.

Shugaban Kungiyar Farfesa Rabi’u Nasiru ya bayyana hakan sa’ilin zantawar sa da manema labarai jim kadan bayan fitowa taron da ta gudanar da membobin ta a harabar Jami’ar da ke Samarun Zariya.

Ya ce, a shekaru da dama da suka gabata gwamnatoci a kasar nan basa ba bangaren Ilimin fifikon da ya kamata da hakan ke haifar da gagarumar koma baya a bangaren.

Kuma kudaden da suke badawa basu kai adadin da ya kamata su bada ba. To wannan abubuwan ya sa Kungiyar ASUU ta shiga wata yarjejeniya da gwamantin wancan lokaci a shekarar 1992 Kuma aka sake yin wata a 2009 kuma ya kamata a ce an sake irin wannan yarjejeniyar bayan shekara Uku, amma yanzu wajen shekaru 11 kenan ba’ a sake ba. wanda a cewar Farfesa Rabi’u koma baya ne ga harkar Ilimi.

Kuma duka tattaunawa da suka yi a baya ta haifar da d’a mai ido, tunda an samu gagarumin canje-canje a jami’oi saboda ta nan ne aka kawo tsarin samar da asusun kula da ilimi ta Tetfund da yanzu shi ke amfanar da makarantu a matakan jihohi da tarayya.

Kuma ya ce, ana cikin haka ne sai aka kawo tsarin biyan albashi na bai daya wato IPPIS wanda Kungiyar ta ASUU ta nuna rashim gamsuwa da shi har ta kai ga shiga yajin aiki. Daga bisani ma gwamnatin ta rufe makarantu saboda barkewar annobar Covid-19 a Najeriya.

Farfesa Rabi’u Nasiru, Ya jaddada cewa ko gwannati ta sake bude makarantu suna nan kan bakan su na cigaba da yajin aiki saboda gaza cimma matsaya da bangaren gwamnati.

Ya yi kira ga gwamanti ta yi kokari ta himmatu wurin zuwa domin a zauna a gano bakin zaren kuma ta bada kai bori ya hau a kan matsayin ta tunda sun samar da nasu tsarin da suke ganin shi ne mafita domin cigaban kasar nan a harkar Ilimi da Najeriya baki daya.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog