Home LabaraiDaukar Aiki: Kamfanin Dangote da Abdussamad BUA suna neman sabbin Ma’aikata

Daukar Aiki: Kamfanin Dangote da Abdussamad BUA suna neman sabbin Ma’aikata

by Dabo Online
0 comments

Daga cikin manyan kamfanonin simiti a Najeriya, Dangote da BUA Group, suna neman sabbin maaikata a wannan zangon.

Kamfanin BUA da Abdussamad Rabiu yake jagoranta yayi shelar neman ma’aikatan ne a shafinsu na Facebook a daren ranar Talata 7 ga watan Agusta 2019.

Kamfanin ya bayyana cewa ga duk mai bukatar yin aiki da su, ya garzaya shafinsu na yanar gizo-gizo. wanda zamu kawo muku a kasan wannan rubutun.

Danna akan tambarin kasa domin shiga shafin neman aikin.

NB: 1. Kamfanin BUA zasu rufe shafin daukar ma’aikatan a ranar Juma’a 9 ga watan Agusta 2019.

2. Zai fi kyau idan aka zargaza shagunan masu kwamfuta ‘Cafe’ domin ingantaccen cika-cike da kamfanin yake bukata.

A nasu bangaren, kamfanin Dangote sun fitar da yacce mai neman zai nemi aiki.

Dannan akan tambarin kamfanin Dangote domin neman aikin.

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00