Kamfanin Lantarki na KEDCO ya na bin Kanawa bashin Naira biliyan 148

Kamfanin dillancin wutar Lantarki na KEDCO yana bin Kanawa bashi Naira biliyan 148 na kudin wutar lantarki.

Kamfanin na KEDCO ya roki mutanen jihar Kano da su sauke nauyin da ya rataya a wuyansu wajen biyan bashin.

KEDCO ta bayyana haka ne ta hannun shugaban sadarwarta, Ibrahim Sani Shawai a ranar Talata inda ya kara da cewa matsalar da suka samu da kamfanin rarraba wutar lantarki na TCN, ya na da alaka da rashin biyan kudin wata-wata da masu amfani da wutar basa yi.

Ya jadda cewa bisa yanayin cigaba da kamfanin yake yi, kamfanin zai samu wata garkuwa idan har al’ummar jihar suka biyasu bashinsu.”
“Karin samuwar wutar lantarkin ta ta’allaka ne akan masu amfani da wutar.”

“Binciko ya tabbatar da gano bashin Naira biliyan 148, wanda KEDCO ta ke bin masu amfani da wutar lantarki a jihar Kano.”

Sai dai ya kara da cewa duk da bashin da suke bin mutanen Kano, kamfanin bazaiyi kasa a gwiwa ba wajen tabbatartuwa samun ingancin wutar lantarkin a jihar.

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.