Home LabaraiMutane 50,000 sun nemi aikin koyarwar da ake neman mutane 1000 a jihar a Lagos

Mutane 50,000 sun nemi aikin koyarwar da ake neman mutane 1000 a jihar a Lagos

by Dabo Online
0 comments

A kalla mutane 50,000 ne suka nemi aikin koyarwa da ake neman mutane 1000 kacal lokacin da gwamnatin jihar Legas ta sanar da shirin daukar Malamai.

Suru Avoseh, ma’aikaci a ma’aikatar aikin gwamnati ne ya bayyana haka, yayin taron bikin sabuwar shekara da Kungiyar cigaban Mata ta Badagry ta shirya a ranar Lahadi.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya ya rawaici cewar; A ranar 11 ga watan nuwanbar 2019, gwamnatin jihar Lagos ta ayyana shirin daukar Malaman makarantar Sakandire 1000 a fadin jihar.

Mista Avoseh yace wasu daga cikin wadanda suka chanchanta sun samu zama don yin jarabawar gwaji.

“Bayan jarrabawar, ana kiran wadanda suka samu nasara, domin yin gwajin ido na ganin ido.”

“Zuwa yanzu, wadanda suka haye dukkanin gwajin, sun fara samun sakonni a cikin wayoyinsu.”

”Tabbas daman ba duk wanda ya nemi aikin ne zai samu nasarar zana jarrabawar ba, kuma ba duk wanda ya haye jarrabawar za’a dauka ba.”

Ya bayyana cewa nan ba da dadewa ba ma’aikatar Ilimin bai daya da ta aikin gwamnati zata fara bawa wadanda suka samu nasara aiki.”

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00