Gidauniyar Hadeeyatul Khair ta na kira ga al’umma dasu tashi da azumi a gobe Alhamis domin neman daukin Allah akan cutar Corona Virus da ta addabi al’ummar duniya.
Shugaban gidauniyar, Dr Mufidah Fari ce ta bayyana a wata sanarwar da ta aikewa DABO FM a ranar Laraba.
“Muna kira ga al’umma da mu tashi da azumi ranar 5 ga watan Maris domin neman taimakon Allah bisa yaduwar cutar Corona Virus.”
Gidauniyar Hadeeyatul Khair, gidauniyar da wasu mata a jihar Kano suka kafa, ta taimakawa mutane musamman mata ta hanyar basu tallafi da jari na sana’o’i.
A watan Fabarairun 2020, gidauniyar ta kaddamar da shirin fara koyar da sana’o’in zamani ga marasa karfi a yunkurin da take na fitar da al’umma daga cikin kangin talauci, kamar yadda shugabar ta bayyana.
Gidauniyar Hadeeyatul Khair da wasu mata a jihar Kano suka kafa ta kai tallafin kayan abinci da tufafi zuwa gidan marayu da gidan yari a jihar Kano.
A ranar 7 ga watan Julin 2019 ne dai gidauniyar ta kai ziyararta ta farko zuwa gidan Marayu dake Nassarawa a jihar Kano, inda suka rarraba kayan abinci, kayan sakawa dama daffafen abinci domin ciyar da mazauna gidan.Kayayyakin sun hadar da Sabulan wanki, Sabulan wanka, Madara, Biskit, Chizi, Lemuka da Gurasa.
