Labarai

Sauki ya samu: Dan Italy da ya shigo da Coronovirus Najeriya ya samu karfin cin ‘amala’ -Likita

Bature dan kasar Italy da ya shigo da cutar Coronovirus Najeriya ya fara samun sauki domin har ya samu kwarin cin ‘amala’. Kamar yadda shugaban dake kula da wajen gwajin masu dauke da cutar Coronovirus ya shaida wa majiyar Dabo FM.

Vanguard ta ruwaito shugaban mai kula da Lagos Biobank, Dr Bankole Akinwale shene ya bayyana haka.

Wannan yana zuwa ne bayan geamnatin jihar Lagos ta bayyana cewa ta killace wasu mutane 2 da ake zargin kamuwa da cutar Coronovirus a wajen binciken ta dake Yaba, a ranar Litinin da Talata.

Haka kuma an sallami wani dan kasar China da akayi zargin yana dauke da cutar bayn an masa gwaje gwaje an tabbatar bashi da ita.

UA-131299779-2