Home Ra'ayoyiBudaddiyar wasika ga gwamnati kan a bude masallatai -Sen Abba Madugu

Budaddiyar wasika ga gwamnati kan a bude masallatai -Sen Abba Madugu

by Muhammad Isma’il Makama
0 comments

Cikin wata wasika daya aikewa Dabo FM, Sen Abba Madugu ya fara da cewa:

Zuwa Ga Gwamnan Jihar Kano
Dr Abdullahi Umar Ganduje CFR Khadimul Islam

Assalamu Alaikum

Me Girma Gwamna dafatan kasha ruwa lafiya Allah ya karbi ibadun mu.

Muna kara godiya da jinjina ga Kokarin da kake dakuma kwamati na cutar suke wajen yaki da wagga cuta ta Koronabairos Allah Kuma Ya kawo mana karkashenta a Kano Da Nigeria baki daya.

Na Rubuta Wagga wasika Don Bada Tawa Gudunmawar Don shawo Kan Wagga cuta Dakuma Masalaha ta halin da muke ciki.

Tunda dai Hana cakuduwar jama’ah ya gagara a kasuwanni,ai yakamata a bude Mana masallatan jumu’ah! Koda na Saa Dayane wato Awa Daya.

Cikin girmamawa ga Mai girma gwamna Khadimul Islam.da Kuma dukkan shugabanni musamman masu Ruwa da tsaki akan wannan cuta ta Korona baros (Covid -19)

Ina Mai bawa gwamnati da jagororin Hana yaduwar wannan Annoba Shawara kan cewar”Kamata yayi a dauki matakan kariya a bude Mana masallatan jumu’ah,duba da Kasuwannin da ake budewa Babu wani Wanda yake daukar matakin kariya Sai dai-dai.

Amma mu masallatan mu muna da Tsarin da duk Wanda yazo a tilastashi Sai yabi qaa’ida ko Kuma a hanashi Shiga kamar yadda lokacin Boko Haram mutane da Kansu suke daukar mataki akan duk Wanda yai turjiya ga jami’an tsaro ko(Yan agaji).

Kuma Ina da kyakkyawan yaqinin Cewa”mutane zasu bi dokar yadda yakamata Kasancewar kowa yasan cutarnan da Kuma illarta.

Ina bada Shawarar a dauki mataki kamar haka
✓Babu mai Shiga Masallaci dole Sai ya saka face mask.
✓Mutum ya saka Handgloves(Safar hannu ta ma’aikatan lapiya)
✓matsa Hand Sanitizer ya mutsstike hannunsa ko asaka omo don wanke Hannu.

Su Kuma hukumomin Masallaci suyi kokarin tabbatar da Wadannan
✓Bayar da tazarar mita biyu tsakanin Kowanne mutum ko Kuma Kowanne Sahu.
✓Kayyade iya adadin Mutanen da Zaa su Shiga Masallaci.
✓Katse duk wata hanya da Za’a iya Shiga Masallaci ba tare da sanin Yan agaji ba.
✓Liman ya takaita khudbah,ya Kuma takaita wajen karatun Sallar.
✓Bayan Idar da Sallah a tabbar ba’a ba da damar cunkoso ba,musamman lokacin fita.

Aikin Yana da wahala Kuma Yana da yawa, Amma ai ladan Sallar jumu’an Ma Yana da yawa Wanda ba zaka kwatantashi da yawan ko wahalar aikin kiyaye dokar ba.

Muna fatan ALLAH yasa muyi sallar jumu’ah cikin Aminci A kwana kusa,gobe dai jumu’ah ta hudu kenan Kuma Azumi Yana sha-biyar.

Muna Addu’ar ALLAH ya kawo Mana saukin wannan Annoba ya yaye Mana ita gabadaya.ya bawa Shugabanninmu damar samawa Al’umma mafita ta Alkhairi.

ALLAH kaji qan mamatanmu da suka mutu a wannan yanayi da wannan lokaci gabadaya.

Abba madugu Dan Jamiyyar APC
07/05/2020
abymadugu@gmail.com

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00