Labarai

Osinbajo ne shugaban kungiyar gajeru ta kasa -El Rufa’i

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El Rufai ya bayyana mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo a matsayin shugaban kungiyar su ta gajeru a fadin Najeriya baki daya.

A wani sakon da ya fitar a shafinsa na Twitter cikin barkwanci, ya bayyana cewa "Mu gajerun mutane muna samun kyakkawan wakilci a kowanne bangare na gwamnatin kasar nan."

El Rufa'i ya mayar da martani ne ga wani mai shirin barkwanci, Gbadewonuola Olateju Oyelakin, wanda akafi sani da Teju Babyface, biyan wani sakon Twitter da ya aike wa gwamnan.

Cikin wata tattaunawa da sukayi tare gwamna El Rufa'i ya bayyana kansa a matsayin sakatare janar na kungiyar.

Ya kara da cewa "sanda nake kan samartaka ta na samu matsaloli wajen yan mata saboda gajerta ta, yawancin yammatan sun fini tsayi."

"Haka dai naci gaba da rayuwa har na samu kyakkyawar mace mai hazaka daga karshe, wadda na fita tsayi da rabin inchi."

Karin Labarai

UA-131299779-2