RAJASTHAN: Hon Muhammad Gudaji Kazaure, dan majalissar tarayya a Najeriya, ya ce matsalar tsaro da ake fama da ita a Najeriya ta fi ta annobar Koronabairas.
Dan majalissar da ke wakiltar kananan hukumomin Gwiwa, Kazaure, Roni, da ‘Yan Kwashi na jihar Jigawa a majalissar wakilan Najeriya, ya ce bai kamata gwamnati ta bai wa yaki da Koronabairas muhimmancin sama da na matsalar tsaro ba.
DABO FM ta tattara cewa dan majalissar ya yi korafin ne yayin zaman majalissar a cikin makon da muke bankwana da shi.
“Ana maganar tsaro wa yake maganar Korona? Mutane nawa Korona ta kashe? A rana daya kadai, wadannan ‘yan ta’adda sun kashe mutane sama da wadanda Korona ta kashe a Najeriya.”
“Bai kamata a dakatar da harkokin rayuwa akan Korona ba. Akan ‘yan ta’addar nan ya kamata ace an rufe garuruka tare da daukar matakan kawar dasu ba akan wata cutar Koronabairas ba.”
Kazalika dan majalissar ya soki jami’an tsaro da cewar ba sa aikin da ya dace duba da a cewarshi yadda ‘yan ta’addar suke dadewa suna aikata ta’addanci.
“Idan har gwamnati za ta mai da hankali akan Koronabairas, me yasa ba ta bai wa matsalar tsaro muhimmanci ba?
