Labarai

Gobara ta tashi a fadar shugaban kasa

An samu tashin gobara a fadar shugaban Najeriya ‘Presidential Villa’ da ke birnin Abuja a ranar Alhamis.

Sai dai babban mataimakin shugaba Muhammad Buhari a fannin yada labarai, Garba Shehu, ya bayyana al’amarin a matsayin dan karami.

Ya kuma alakanta tashin gobara da wani tartsatsin wutar lantarki da ya auku, kamar yadda Daily Trust ta rawaito.

DABO FM ta tattara cewar Mallam Garba Shehu ya bayyana cewar gobarar ta tashi a ranar Alhamis a wani sito na kusa da wani dakin ibada na cikin fadar gwamnatin.

Ma’aikatan bada agajin gaggawa sun samu shawo kan al’amarin da ya faru wanda tartsatsin wutar lantarki ya haifar. Sun yi amfani da durakun kashe gobara da suke jingine a ofishin kashe gobara da yake a wajen fadar nan.

“Mun yi sa a, ba a samu wanda yaji ciwo ko mummunan rauni ba.”, inji Mallam Garba Shehu.

Karin Labarai

UA-131299779-2