Home LabaraiNNPC ta fara ginin katafaren asibiti da zai laƙume biliyan 21 a Katsina

NNPC ta fara ginin katafaren asibiti da zai laƙume biliyan 21 a Katsina

by Dabo Online
0 comments
Mele Kyari - Daraktan NNPC

RAJASTHAN: Babban daraktan NNPC, Mallam Mele Kyari, a ranar Asabar, ya kaddamar da fara ginin asibiti mai gadaje 200 da zai kula da cututtuka da ke yaduwa tsakanin jama’a a garin Kaita ta jihar Katsina.

Asibitin mai gadaje 200 da zai lakume Naira biliyan 21 zai kasance mai bayar da agajin gaggawa ga yankin arewa maso yammacin Najeriya.

Asibitin ya kasance da ya daga cikin asibitoci 12 da NNPC ta gina a dukkanin yankuna 6 da ke Najeriya.

Babban daraktan ya bayyana cewar za a kammala ginin asibitin cikin watanni 18 tare da cewar biliyan 21 da aka ware wajen gina asibitin ta kunshi samar da kayayyakin aiki tare da kula da walwalar marasa lafiya a asibitin.

“Katsina ta kasance jiha daga cikin jihohi 12 da aka zaba domin yin wannan aikin na jinkan al’umma domin yakar cutar Kwabid19 da kuma wasu cututtukan da za a iya samu a nan gaba.”

“Muna yin irin wadannan ayyuka a jihohi 12 a na sassan yankunan Najeriya, kuma gwamnatin Najeriya ce take daukar nauyin wadannan ayyuka ta hanyar NNPC.”

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00