Home LabaraiWasu jihohin su na cogen adadin masu Korona – El-Rufa’i

Wasu jihohin su na cogen adadin masu Korona – El-Rufa’i

by Dabo Online
0 comments
Nasiru El-Rufai

RAJASTHAN: Gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasiru El-Rufa’i, ya bayyana cewar akwai gwamnoni da ke cogen adadin wadanda cutar Kwabid19 ta kama a jihohinsu.

Gwamnan ya bayyana haka ne cikin wani martani da yake yi a shafin Twitter bayan da wani ya yi tsokaci kan cewar jihohi ne suke saita alkaluman da suke so hukumar NCDC ta bayyana.

“Wasan Lambobi, a kowanne dare, hukumar NCDC ta na fitar da masu dauke da Kwabid19, to me suke nufi? Kwamitocin da ke karkashin ikon gwamoni ne suke aike da gwaji zuwa dakunan bincike. Dakunan binciken nan suna bincikar abinda aka aike musu ne kawai. Wanda yake da ikon daukar samfuri, shi ne yake da ikon saita adadin da yake so.

“Gwamnoni su na son lambobi marasa yawa.”

Da yake matani akan bayanan sama, gwamna El-Rufa’i ya ce jihar Kaduna da wasu ba sa daga cikin jihohin da suke yin irin wannan cogen saboda suna bin diddigin wadanda suka kamu da cutar ta Kwabid19.

“Eh ka dan yi daidai, amma ba dukkannin jihohi bane suke son adadin mara yawa na ‘bogi’ ba. Abuja, Kaduna da Legas su na bin diddigi saboda muna son fitar da adadin wadanda suka kamu na ainahi domin basu kulawa.

DABO FM ta tattara cewar zuwa yanzu, ranar L:ahadi , 7 ga Yuni 2020 da misalin 8:50 na safe agogon Najeriya ta jihar, mutane 337 ne suka kamu da cutar Kwabid19 a jihar Kaduna.

Jumillar wadanda suka kamu a Najeriya, 12,233.

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00