Home LabaraiBaza mu kuma lamuntar shiru da rashin daukar mataki kan kashe-kashe ba -Sarkin Musulmi

Baza mu kuma lamuntar shiru da rashin daukar mataki kan kashe-kashe ba -Sarkin Musulmi

by Muhammad Isma’il Makama
0 comments
Sarkin Musulmi Saad III

Sarkin musilmi, Sultan Abubakar Sa’ad III ya bayyana bazai kara lamuntar rashin daukar mataki tare da shirun gwamnati kan kashe-kashen dake afkuwa a arewacin Najeriya ba.

Rahoton DABO FM ya bayyana sarkin wanda shine shugaban Jama’atul Nasurul Islam kuma sarkin musulmi na Najeriya na yin alawadai da rashin tabuka komai na gwamnati da jami’an tsaro wajen hare haren yan Boko Haram, tare da garkuwa da mutane.

Ya kuma bayyana cewa gwamnatin tarayya data jiha baki daya ya kamata su dauki aikin da aka zabe su akai na kare dukiya da rayukan mutane.

Sultan Abubakar III, wanda ya bayyana hakan ta bakin sakatare janar na kungiyar JNI, Dr. Khalid Abubakar-Aliyu ya bukaci musulmi da su fada cikin addu’o’i da nafilfili domin kawo karshen kashe-kashe a fadin kasa baki daya.

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00