Home LabaraiKisan kiyashi a Arewa: Sule Lamido ya caccaki Buhari

Kisan kiyashi a Arewa: Sule Lamido ya caccaki Buhari

by Dangalan Muhammad Aliyu
0 comments

Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, ya mayar wa shugaba Muhammadu Buhari martani akan bayanan shugaba Buhari ya rokon mutanen Katsina su yi hakuri sakamakon kashe-kashe da suke faruwa a jihar.

Alhaji Sule Lamido ya yi martanin ne a shafinsa na Twitter, in da ya nuna cewar bai kamata Buhari ya bai wa mutanen da suka yi murna da samun nasararsa hakuri ba a lokacin da suke fama da kashe-kashe.

“Ba rokonsu za kayi ba.”

Sun roke ka, sun yi wa wadanda suke yi maka hamayya barazana, Malamai sun yi huduba a masallatai tare da yi wa ‘yan uwansu Musulmai barazana da shiga wuta ga wadanda basu goyi bayanka ba.

“Matasa sun hada maka gudunmawar kudin don yakin neman zabe, wasu daga cikinsu har ruwan kwatami suka sha, wasu suka mutu wajen yin murnar samun nasararka.”

DABO FM ta tattara cewar bisa rahotanni da aka fitar a ‘yan kwanakin nan da muke ciki an kashe a kalla mutane 200 a kashe-kashen ‘yan Bindiga a jihar Katsina da hare-haren mayakan Boko Haram a Borno.

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00