Home LabaraiZulum yaki karbar bulo mara inganci a inda ya bada kwangilar ginin gidaje 500

Zulum yaki karbar bulo mara inganci a inda ya bada kwangilar ginin gidaje 500

by Muhammad Isma’il Makama
0 comments

Gwamnan jihar Barno, Babagana Umara Zulum yaki amincewa da bulo mara ingancin a garin Auno inda ya bada kwangilar ginin gidaje 500.

Rahoton DABO FM ya bayyana gwamnan cikin wata ziyara da ya kai bangaren da ake wannan ginin gidaje, kamar yadda kafar ofishin gwamnan ta fitar a ranar Asabar wanda take ya bada umarnin a sauyo masa duk wani bulo mara inganci.

Garin Auno dai na kan hanyar Maiduguri zuwa Damaturu wanda ke karkashin karamar hukumar Kunduga wanda gwamnan ke rangadin duba aiyukan wannan karamar hukuma dama kewayen cikin garin Maiduguri.

Haka kuma Zulum ya ziyarci wajen da gwamnatin sa ta bada aikin ginin dakunan dalibai dake jami’ar jiha ta Maiduguri tare da duba wani aikin da aka kammala a sakandaren Moramti Mega.

Wannan na zuwa ne bayan gwamnan ya dawo garin Maiduguri daga garin Abuja inda ya gana da shugaban kasa, Muhammadu Buhari tare da ministocin walwala da jin kai, Sadiya Umar Faruk, Ministan Gona, da shugaban hukumar ‘yan gudun hijira.

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00