Babban Labari Manyan Labarai

Zargin rashin kula da lafiya: Kaftin Zakari ya nesanta kansa daga labarin da aka buga a kan sa

Tun bayan zantawar da wani Jami’in rundanar sojin Najeriya mai suna Kaftin Zakari Sani, ya yi inda ya roki gwamantin tarayya da rundunar sojin Najeriya domin kawo masa dauki bisa lalurar da yake ciki tun bayan harin da wasu fulani suka kai ma ayarin su a Jihar Benue, yanzu haka labarin da ke shigo mana na nuna cewar rundunar sojin ta dauki matakin cigaba da kula lafiyar sa. Inda yanzu haka aka kwantar da shi a wani asibiti a babban birinin tarayya Abuja.

Sai dai tun bayan daukan wannan mataki, sai ga wani labari da yake zuwa a yammacin lahadin nan, da ke nuna cewar har yanzu Kaftin Zakari Sani na bukatar tallafin rundunar sojin.

Jin haka ke da wuya, sai Dabo FM ta tuntubi Kaftin Zakari Sani domin Jin gaskiyar zancen, inda ya bayyana mana cewar, shi yanzu haka yana samun kulawar ta musamman a wani kasaitaccen asibiti, wanda kuma rundunar sojin Najeriya ce da kanta ta dauki nauyin kula da lafiya sa.

Sai dai ya daura alhakin cigaba da yada labarin zuwa ga wasu kafafen yada labarai da cewa wasu ne da ke nufin sa da sharri domin dakile kokarin da rundunar sojin ke yi a kan sa ke yada labarin.

A zantawar sa da Dabo FM a kwanakin baya, ya yi mana bayani kan wata takardama da ta taso
tsakanin sa da wani abokin aikin sa mai suna Kaftin Alibaba, wanda yake zargin ya turo wasu yan daba su ci zarafin sa har kofar gida.
tun bayan wata rashin fahimta da ta taso tsakanin shi Kaftin Alibaba da tsohuwar matar sa wanda kuma ‘yar uwa ce ga shi Kaftin Zakari Sani, har ta kai ga saki Uku tsakanin su.
Bisa wannan takaddama ce, ya ce yana zargin wasu na kusa da Alibaba ke yada labarai karya a kansa.
Inda ya roki Jama’a su yi watsi da duk wata sanarwa da ba daga bakin sa ta fito ba.

Kaftin Zakari Sani, ya gode ma rundunar sojin Najeriya da shugaban rundunar Tukur Yusuf Buratai bisa daukar matakin cigaba da kula da lafiyar sa cikin gaggawa.

Karin Labarai

UA-131299779-2