Home LabaraiGwamnatin Jigawa za ta shuka bishiyoyi miliyan 2.5

Gwamnatin Jigawa za ta shuka bishiyoyi miliyan 2.5

by Dabo Online
0 comments
Badaru Abubakar

Gwamnatin jihar Jigawa karkashin gwamna Badaru Abubakar, ta bayyana kudirinta na shuka bishoyoyi miliyan 2.5 a fadin jihar.

Gwamnatin ta ce ta zata shuka bishiyoyin ne domin kare kasar noma a jihar daga komawa hamada.

Mai magana da yawun Ma’aikatar Muhalli ta jihar, Zubairu Sulaiman ne ya sanar da haka, in da ya bayyana cewa zasu raba wa al’ummar jihar iri kyauta domin su shuka a gidaje da gonakinsu.Ka

Kazalika ya ce za a kaddamar da shirin a cikin watan Yuli a fadin kananan hukumomin jihar 27, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ‘NAN’ ya rawaito.

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00