Mai unguwar garin Batsari da take karamar hukumar Batsari ta jihar Katsina, Alhaji Muhammad Mu’azu ya bayyana cewa harin ‘yan Binduga a unguwar ya yi illar da sun samu marayu 1600 da Zawarawa 500.
Mai unguwar ya bayyana haa ne cikin wata hira da yayi da jaridar PUNCH.
Da yake amsa tambayar adadin mutanen da aka yi rashin a yankin nashi, ya shaida cewa rashin da aka samu yana da yawa adadin da baza a iya kayyadewa ba.
“Ba za a iya zayyana adadnin rashin ba. Ba zan iya kayyade rashin da akayi idan aka kwatanta su da kudi ba. Sai dai zance asarar sai dai a kirga miliyoyi. Misali, nawa ne zai iya dawo da wadanda ‘yan bindigar suka kashe? Ba za a taba iya kimanta rashin dan adam 1 da kudi ba.”
“Mun rasa mutane sama da 300 a hare-haren ‘yan bindiga. ‘Yan bindiga sun karkashe mana mutanen da basu ji ba basu gani ba. Sun kashe mana maza da mata. Musamman da suka kashe a kalla maza 300. Saboda mutuwarsu a yanzu muna da a kalla zawarawa 500 da marayu 1600.”
“Har makarantar da ‘yan gudun hijira suke ciki, itama ‘yanm bindigar basu bar ta ba.
“Baya ga matsa mana a al’amuranmu na noma, ‘yan ta’addar nan sun sace mana shanu a kalla miliyan 3 ko 4 wadanda yawancinsu bujumaye ne. Yaranmu a yanzu basa zuwa makaranta a dukkanin wurare da ‘yan bindigar suka kai hari saboda tsare rayukansu. Wasu daga cikin yaran sun yi balaguro zuwa wajen da suke ganin yafi salama.”
