Yanzu haka asibitin koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Shika Zariya ta dukufa wurin bunkasa kiwon lafiyar al’umma, da zama daya tamkar da dubu wurin gudanar da harkokin ta a matsayin ta na daya daga cikin manyan asibitocin kasar nan da gwamanti ke alfahari da ita.
A zantawar sa da Dabo FM a ofishin sa, Shugaban Asitin Farfesa Hamidu Ahmad Umdagas, ya bayyana cewar tun zaman sa shugaban Asibitin a shekarar da ta gabata, an samu gagarumar nasara a sha’anin gudanarwar Asibitin da ba za’a iya mantawa da su ba.
A matsayin Asibitin koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello Shika Zariya, da aka samar tun shekaru da dama da suka wuce, zuwa yanzu hobbasan da ake ya zama abin alfahari da tunkaho ganin yanayin jagorancin da a ke yanzu haka.
A cewar Farfesa Hamidu Ahmad, wasu daga cikin nasaroron da aka samu a Asibitin sun haka da samar da karin katafaren dakin kula da marasa lafiya cikin gaggawa (Emergency) domin rage cunkoson da ake samu a tsohon da ake da shi.
Kuma sun yi fadi tashin ganin gwamnati ta amince sun dauki ma’aikata da za su maye gurbin wanda suka aje aiki ko suka canza wuraren aiki ko kuma suka rasa rayukan su.
Hakan kuwa na da nufin samar da karin ma’aikatan jinya da za su cigaba da samar da kulawa ga marasa lafiya da suke zuwa Asibitin daga sassan kasar nan a kullum rana.
A bangaren tsaftar muhalli kuwa, a cewar Farfesa Hamidu, tun a tsawaon lokaci, an san harabar Asibitin na fama da wari saboda sinadaran da ake amfani da su wurin tafiyar da lamuran yau da kullum, yanzu haka bisa wasu kudade da suka samu daga bangaren gwanati sun dauki ragamar kawar da wannan wari, kuma sun yi nasara da yanzu mahalarta za su iya shiga Asibitin su fita ba tare da sun ji wani wari da zai kawo masu cikas wurin tafiyar da harkokin su ba. Kuma a cewar shi farawa ne domin suna da tsare-tsare da ake sa ran zai kara kai Asibitin zuwa ga tudun mun tsira.
Baya ga nan, akwai aikin katafaren gyaran dakunan kwanan majinyata da ofisoshin ma’aikata da ake yanzu haka.
Kuma bisa jagorancin sa, akwai manyan naburorin kula da marasa lafiya wanda wasu ma babu irin su a fadin kasar nan.
Asibitin koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello Shika, na da tsawon akalla kilomita Daya da d’go Uku ne, Wanda a da idan aka shiga musamman da dare, Asibitin na fama da duhu saboda rashin fitillu da zai haska sassan Asibitin, amma yanzu haka a cewar Farfesa Hamidu Umdagas, sun sanya manyan fitillu masu aiki da hasken rana da za su kara inganta sha’anin tsaro da gudanarwar Asibitin.
Daga nan sai ya gode ma Shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamanan Jihar Kaduna Malam Nasiru El-rufa’i saboda cikakken hadin kai da goyon baya da suke ba Asibitin domin ta cigaba da rike matsayin ta na babbar Asibitin da al’ummar Arewacin Najeriya su ke alfahari da ita.
Kuma ya gode ma daukacin membobi kwamitin gudanarwar Asibitin da masu taimaka masa a fannonin daban-daban da kuma Sarakuna iyayen kasa musamman Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris bisa aikin da suke ba dare ba rana domin cigaban Asibitin.
