2
Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta jihar Kano ‘KUST’ ta dakatar da ɗalibanta 10 da aka samu da hannu a cin zarafin wata ɗaliba.
Hukumar ta ce kuma tana cigaba da gudanar da bincike, ta sanya gobe Alhamis a matsayin ‘Ranar Abaya’.
Shugaban kungiyar tsofaffin ɗaliban jami’ar, Suhailu Sabo Maccido ne ya tabbatar da lamarin a yayin zantawarshi ta wayar tarho da Jaridar Sahelian Times.
Kazalika shugaban ɗaliban jami’ar, Kwamared Uwaisu Ibrahim Babba, ya tabbatar da dakatar da jami’ar da yi wa ɗaliban su 10.
..
