Labarai

Hukumar yaki da rashawa ta shiga binciken fai-fan bidiyon dala na Ganduje cikin gaggawa

Hukumar yaki da rashawa ta jihar Kano ta kafa kwamiti na binciken gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje cikin gaggawa.

Majiyar DABO FM ta jiyo shugaban hukar na jihar Kano, Muhuyi Magaji Rimingado yammacin Laraba inda ke bayyana hakan bayan kiraye kiraye da wasu kungiyoyi suka kai gaban hukumar. Kamar yadda jaridar Solacebase ta fitar.

Hukumar ta bayyana tini ta kafa kwamiti da zai kara bincike na tsanaki akan wannan batun. Sai dai kuma yan siyasa na ganin kamar wata dabara ce ta kauda hankalin alummar jihar bayan tsige Sarki, Muhammadu Sanusi, kana kuma suna ganin hukumar ma gwamnan ke juya ta.

Karin Labarai

UA-131299779-2