Labarai

Najeriya zata hana shigo da injin Jannareta, tare da daurin shekaru 10 ga duk wanda ya siyar

Bina Enagi, Sanata mai wakiltar kudancin jihar Neja a majalisar dattijai ya shigar da wani kudiri na Najeriya ta hana shigo da injin bada hasken wutar lantarki tare da daurin shekaru 10 ga duk mai kunnen kashin da ya sayar wa yan Najeriya.

Majiyar DABO FM ta bayyana kudin wanda ya samu damar tsallake karatun farko a majalisar a Laraba na kunshe da hana amfani da duk wani nau’in injin jannareta.

A halin yanzu dai Najeriya na samun karfin wutar lantarki 4000mw, inda take rabarwa da alummar kasar fiye da miliyan 200 hasken wutar lantarki mai yawan 3000mw kacal. Kamar yadda TheCable ta first.

UA-131299779-2