Labarai

Ranar Tarihi: Shugaban karamar hukumar Zariya ya gabatar da kasafin shekarar 2020 a gaban Kansiloli

A karon farko a tarihi, majalisar mulki ta karamar hukumar Zariya dake Jihar Kaduna, ta gabatar da kasafin kudin shekarar 2020 a gaban majalisar kansilolin karamar hukumar.

Da yake gabatar da kasafin kudin a rubuce a ranar Alhamis din nan, shugaban karamar hukumar, Injiniya Aliyu Idris Ibrahim, ya yi takaitaccen bayanin yadda aka samu kudaden tare da kashe wa a shekarar 2019 da ta gabata.

Wakilin DABO FM da ya halarci zaman, ya tabbatar da shugaban karamar hukumar ya mika kumshin kasafin shekarar 2020 da ake fuskanta da ya kai na sama da naira Biliyan 3.

Takardar, dauke da sa hannun mataimakin daraktan kasafi na karamar hukumar, Shuaibu M Bello, a madadin shugaban, An gabatar da ita ce a yayin zaman majalisar, bayan da kakakin Majalisar Hashimu Bako Wadata, ya naimi sanin ko akwai wani sako da aka samu daga bangaren zartaswa.


Sai Kansila mai wakiltar gundumar Kaura kuma mataimakin shugaban masu rinjaye Hon Salisu Skipper ya bayyana cewa, kamar yadda aka bukata a zaman da ya gabata, majalisar zartaswa ta aiko da rubutacciyar takarda kumshe da daftarin kasafin kudin.

Sai dai abun da ya dauki hankali tare da jawo zazzafar muhawara tsakanin ‘yan majalisar, shi ne yadda aka gabatar da takardar a rubuce, mai-makon yanda suka bukata tun da farko.

Kansila mai wakiltar gundumar Tukur-tukur Hon Isma’ila Shu’aibu, ya fara nuna damuwar sa tare da watsi da matakin da aka bi wurin gabatar da kasafin kudin, yayin da ya samu goyon bayan kusan dukkanin Kansilolin akan wannan matakin.

Bayan doguwar tattaunawa akan wannan batu, majalisar ta samu matsaya kan dole a koma a dubi kasafin kudin shekarar 2019 data gabata, sannan a koma da takardar da aka turo domin sake naiman shugaban karamar hukumar ko Daraktan kasafi ko Daraktan Kudi ko kuma wani babban jami’i daga karamar hukuma, ya zo ya gabatar da kasafin kudin a rubuce kuma a bayyane.

A gefe guda kuma, majalisar ta karbi rahotan Kwamitin da aka kafa domin zagayawa tare da duba wasu muhinman ayyukan da karamar hukuma ta gabatar a kasafin kudin shekarar da ta gabata.

Shugaban kwamitin Hon Abubakar Abdullahi Muhammad, wanda mataimakin shugaban kwamitin, Hon Yusha’u Muhammad ya gabatar a madadin sa, ya ce, zagayen nasu ya gano wasu tarin matsaloli a aikace-aikacen da aka yi a wasu gundumomi kamar Tudun Wada, Dambo da kuma Wucicciri.

Yayin da kwamitin ta bada shawarar tsawatarwa wasu daga cikin ‘yan kwangilolin da suka gudanar da wasu daga cikin ayyukan, kuma kwamitin ya naimi majalisar zartaswa ta gaggauta biyan ‘yan kwangilolin hakkokin su.

Sai dai daga bisani, majalisar ta amince da rahotan Kwamitin, kuma ta naimi akawun majalisar ya rubuta takarda dauke da korafe-korafen abubuwan da suka gani a zagayen da suka yi.

Masu Alaka

Akwai lauge cikin nadi a batun tsige shugaban karamar hukumar Zaria -Sarkin Gandun Zazzau

Mu’azu A. Albarkawa
UA-131299779-2