Labarai

Abdussamad Bua ya bayar da kyautar Naira biliyan 1, kayayyakin aiki don yakar Coronavirus

Shugaban kamfanin BUA Group, Alhaji Abdussamad Isiyaka Rabi’u ya bayar da tallafin Naira biliyan 1 ga gwamnatin tarayyar Najeriya domin yakar cutar Coronavirus da ta barke a kasar.

A sanarwar da kamfanin BUA ya fitar ga manema labarai a shafinsu na yanar gizo-gizo ranar Alhamis, tace tallafin ya hada da bayar da kayayyakin aikin lafiya tare da na’urorin gwaje-gwaje wadanda zasu taimakawa gwamnatin Najeriya domin yakar cutar.

“Kyautarmu zuwa gwamnati da hukumar dake kula da cututtuka bazai tsaya a iya bayar da tallafin kudi ba, zai kunshi taimakawa bangaren lafiya da kare ma’aikatan da suke kan gaba wajen yakar wannan annobar.”

DABO FM ta tattara cewar Abdussamd Bua yace tini dai nan ba da dade wa ba kayan aikin da ya siyo zasu shigo Najeriya inda yace jihohi 9 zasu amfana da kayayyakin da zai raba.

“Baya ga tallafin kudin, mun siyo kayayyakin aiki da zamu jihohi biyu manyan dake arewaci da kudancin Najeriya. Mun sake zabar jihohi guda 7 daga kowanne sashin Najeriya.”

Yace tallafin kudin zai zowa gwamnatin ne ta hanyar babban bankin CBN a wani kwamitin yaki da Coronavirus na masu zaman kansu.

“Daga cikin jihohi 9 da muka zaba, kowacce zata samu makarin fuska guda 100,000, tabarau na kariya guda 2000, safa guda 1000, kayayyakin gwaje-gwaje guda 1000 da sauransu.”

DABO FM tattara cewar jihohin sun hada da jihar Kano, Legas, Adamawa, Edo, Kwara, RIvers, Abia, Akwa-Ibom da jihar Sokoto.

UA-131299779-2