//
Sunday, April 5

Covid-19: Ganduje ya sanya dokar hana shiga ko fita daga Kano ta kowacce hanya

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje ya sanya dokar hana shiga ko fita cikin jihar ta kowacce hanya daga ranar Juma’a mai zuwa.

Gwamnatin ta haramta shige da fice cikin jihar ta hanyoyin da suka kunshi iyayokin kasa na titin mota, jirgin sama da dukkanin sauran hanyar da take bayar da dama a shiga jihar Kano.

A wata sanarwar da mataimakin gwamnan a fanni labarai Salihu Tanko Yakasai, yace gwamnatin ta dauki matakin ne domin kariya daga shigar cutar CoronaVirus cikin jihar.”

Ga cikakkiyar sanarwa;

“Mai Girma Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje OFR ya bada umarnin rufe duk hanyoyin shigowa jihar Kano ciki harda filin jirgin sama na Mallam Aminu Kano daga ranar juma’ah mai zuwa, wato 27 ga watan March sha biyun dare. Duk wanda ya taso daga wata jiha ko kuma yake san barin Kano toh yayi kokari ya shigo tsakanin gobe alhamis da kuma jibi juma’ah.

Masu Alaƙa  Kano: Wadanda babu zargin cin hanci da rashawa akansu ne zasu zama kwamishinoni - Ganduje

Gwamnati ta dau wannan mataki ne domin kare al’ummar jihar Kano daga kamuwa da wannan cutar corona wato Covid-19 da ake fama da ita a duniya baki daya. Kawo yanzu dai ba wanda ya kamu da cutar a jihar Kano.”

Karin Labarai

Share.

About Author

Comments are closed.

%d bloggers like this:
DABO FM 2020