Abubuwan da suka faru a Rana Irin ta Yau, 1 ga Oktoba a fadin Duniya

dakikun karantawa

Ranar 1 ga Oktoban shekarar 1960 Najeriya ta samu ‘yancin kai daga hannun Birtaniya. Najeriya dai tana da kabilu fiye da 300 inda itace a matsayi na 3 a yawan kabilu a fadin Duniya.

A ranar 1 ga oktoban shekarar 2015 an siyar da Dalar Amurka $1 a dai-dai da Naira 199.

A ranar 1 ga watan Oktoban shekarar 1977 dan kwallon kasar Barazil Pele ya kawo karshen rayuwarsa ta kwallo. Ya ci kwallaye dubu 1 da 281 a gasa dubu 1 da 363 da ya halarta.

A ranar 1 ga Oktoban shekarar 1880 Thomas Edison ya bude kanfanin kwan wutan lantarki na farko a duniya.

A ranar 1 ga watan Oktoban shekarar 1939 ‘Yan Nazi suka shiga birnin Woso bayan sun yi wata guda suna fafatawa da sojojin Polan.

A ranar 1 ga watan Oktoban shekarar 1946 Kotun Numberg ta yanke wa ‘Yan Nazi guda 12 hukuncin kisa yayinda aka yanke wa Rudolf Hess hukuncin rai da rai a gidan yari.

A ranar 1 ga watan Oktoban shekarar 1960 a kafa sabuwar hukuma a Saiparas bayan kasar ta samu ‘yancin kanta daga wurin Ingila.

A ranar 1 ga watan Oktoban shekarar 1992 ‘Yan Ta’addan PKK suka kai hari birnin Bitlis inda suka kashe mutane 37 wadanda cikinsu hada yara da mata inda kuma suka jikkatar da mutane 20.

A ranar 1 ga watan Oktoban shekarar 1995 aka yi girgizar kasa mai girman ma’aunar Richter 6.1 a birnin Afyon dake Turkiyya inda mutane 90 suka rasa rayukansu yayinda gine-gine sama da dubu 14 suka lalace.

A ranar 1 ga watan Oktoban shekarar 1998 Firaministan Turkiyya Mesut Yilmaz da Shugaban Rundunar Sojojin Kasa na Turkiyya Atilla Ates suka gargadi Siriya da cewa su dakatar da taimakon da suke ba wa ‘Yan ta’addan PKK.

A ranar 1 ga watan Oktoban shekarar 1999 aka yi “Yakin Chechnya na 2” tsakanin Rasha da ‘Yan Chechnya.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog