//
Wednesday, April 1

Rundunar ‘Yan Sandan Kano tace tana maraba da masu sha’awar shiga ‘Cell’ domin shakatawa

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya reshen jihar Kano, ta bayyana cewa tana maraba da masu sha’awar shiga ma’ajiyar masu laifi a ofishin ‘yan Sanda domin shakatawa.

Kakakin rundunar yan sanda ta jihar Kano Abdullahi Haruna ne ya bayyana haka cikin shirin ‘Yan Sanda da Jama’a na gidan rediyon Dala FM dake jihar Kano.

Dabo FM ta tattaro cewa; Kakakin rundunar ya tattaunawa batutuwa na shirin gyare-gyare a rundunar yan sanda.

Sakamkon gyare gyare da rundunar yan sanda ta aiwatar a dakunan ajiye masu laifuka a chaji ofis dake Kano da kewaye, rundunar ta ce tana maraba da masu shaawar shiga domin yada zango ko shakatawa.

Masu Alaƙa  Kwamishinonin 'yan sanda 13 sun samu karin matsayi zuwa mataimakan babban Sifeta

Mai magana da yawun rundunar na jihar Kano, DSP Haruna Abdullahi, ya bayyana cewa yin hakan yana daga cikin wani matakin gyara da rundunar takeyi domin inganta rayuwar wadanda suke ajiye a wajen suke jiran Shari’a yayin da ake tuhumarsu.

Shirin na wannan rana ya karbi bakuncin sashen bincikar manyan laifuka wato SARS, domin amsa tambayoyi akan irin ayyukan da suke aiwatar wa.

Karin Labarai

Share.

Comments are closed.

%d bloggers like this:
DABO FM 2020