//

Tarihi: Jerin Gwarazan da Kano ta rasa a watan Afrilu

dakikun karantawa

Ranar 4 ga 4, itace ranar da a Kano ba za a manta da ita ba sakamakon rashin wasu daga cikin gwarzaye ‘yan asali jihar da suka koma ga mahalicci mai yin yadda yaso a lokacin da ya so.

DABO FM ta tattaro gwaraza guda 5 da Kano ta rasa a cikin watan Afirilu. Mutanen da suke gwaraza a bangarorin rayuwa daban daban da suka hada da addini, kasuwanci, koyarwa da siyasa.

Zamu tattaunawa akan marigayi Sheikh Ja’afar Mahmud Adam, Mallam Aminu Kano, Dr Muhammadu Adamu Dan Kabo, Dr Habibu Gwarzo da Alhaji Abubakar Rimi.

Dr Habibu Gwarzo (1937 – 2020)

Ya rasu a yau Asabar 4 ga watan 4 2020. Ya kasance fitaccen malamin makaranta wanda tarihi ya nuna ya koyar da wasu daga cikin shuwagabannin Najeriya da suka hada da Janaral Sani Abacha da Janaral Ibrahim Badamasi Babangida.

Dr Habibu ya rasu a asibitin koyarwa na Mallam Aminu Kano dake a birnin Kano.

Mallam Aminu Kano (1920 – 17 ga Afirilun 1983)

An haifi marigayi Mallam Aminu Kano a 1920, shekaru 40 kafin samun ‘yancin Najeriya. Ya kasance daya daga cikin jagororin nemawa talakan Najeriya hakki daga masu mulkin kama-karya.

Ya kasance malamin addinin Islama, hakan ta sanyashi zama mai bayar da fatawa a bangaren shari’a. Hakazalika malami ne a ilimin Boko wanda ta kai ga ya kafa kungiyar malaman arewa ta farko a tarihi bayan dawowarshi daga makaranta a kasar Burtaniya.

Mallam Aminu Kano ya kasance dan jami’iyyar Mutanen Arewa wacce ta rikide ta koma NPC, ‘National People’s Congress’ kafin daga bisani ya jagoranci bangaren da suka balle daga jami’iyyar zuwa kafa sabuwar jami’iyyar NEPU.

Mallam Aminu Kano ya rasu ranar 17 ga Afrilun 1983.

A Kano, an sanya sunan Mallam Aminu Kano a babban filin tashi da saukar jiragen sama na Kano, babban asibitn koyarwa dake Kano, babbar kwalejin koyan ilimin addinin Musulunci da Shari’a dake Kano, da sauransu.

Dr Muhammadu Adamu Dan Kabo (1942 – 4 ga Afrilun 2002)

An haifi Jarman Kano, marigayi Alhaji Dr Muhammadu Adamu Dan Kabo a ranar 4 ga watan 4, 1942, ya kuma koma ga Allah a ranar 4 ga watan 4 a 2002.

An haifeshi a karamar hukumar Kabo dake arewacin Kano.

Kafin rasuwarshi ya kasance Jarman Kano kuma daga cikin manyan attajirai a jihar Kano da ma Najeriya baki daya.

Ya kasance shugaban kamfanin jiragen sama na KaboAir da yayi shura a jerin jirage mallakin ‘yan Najeriya.

Sheikh Ja’afar Mahmud Adam (1960 – 13 ga Afirilun 2007)

An haifi marigayi Sheikh Ja’afar Mahmud Adam a ranar 12 ga watan Fabarairun 1960, shekarar da Najeriya ta samu ‘yancin kai.

Kafin rasuwarshi, ya kasance fitaccen malamin addinin Musulunci wanda yayi shura wajen karantar da addinin Islama bisa tsarin Salafiyya.

Ya kasance daga cikin malaman da suka yada da’awar kungiyar Izalatul Bidi’a wa Iqamatussunah, kungiyar da ta samu dumbin magoya baya tin bayan kafuwarta.

Ya rasu a ranar 13 ga watan Afrilin 2007 bayan da wasu ‘yan ta’adda suka far masa da harbi yayin da yake limancin Sallar Asuba a masallacinshi dake jihar Kano.

Sai dai a shekarar 2020, shugaban kungiyar ta’addanci mai lakanin Boko Haram, Abubakar Shekau, yayi wasu kalamai da sukayi nuni da daukar alhakin kisan malamin da kungiyar tayi a yayin da take yi wa Dr Isa Ali Pantami barazana.

A jihar Kano, an sanya sunan Sheikh Ja’afar a wani katafaren titi mai kyan gaske.

Alhaji Muhammad Abubakar Rimi (1940 – 4 ga Afrilun 2010)

An haifi marigayi Muhammad Abubakar Rimi a karamar hukumar Sumaila dake Kano cikin shekarar 1940.

Rimi, toshon gwamnan jihar daga 1979 zuwa 1983, ya kasance fitaccen dan gwagwarmayar siyasa nemawa talaka ‘yanci.

A ranar 4 ga watan 4, gwarzo Rimi ya rasa ranshi sanadiyyar bugawar zuciya sakamakon tare shi da wasu yan fashi sukayi a kan hanyarshi ta komawa Kano daga jihar Bauchi.

A jihar Kano, an sanya sunan Abubakar Rimi a babbar tashar talbijin mallakar gwamnatin jihar Kano ‘ARTV’.

Karin Labarai

Dangalan Muhammad Aliyu

•Sublime of Fagge's origin.
•PharmD candidate

Sabbi daga Blog