Labarai

Kotu a Bayelsa ta yanke wa matashi Dahiru ‘Yellow’ hukuncin daurin shekara 26 a yari

Wata babbar Kotu dake da zamanta a jihar Bayelsa, ta yankewa matashi Dahiru Yellow hukuncin zaman gidan gyaran hali har tsawon shekaru 26.

Kotun da take birnin Yenagua a karkashin alkali Inyang Jane tace ta kama matashin da laifuka guda 5 wadanda suka hada da satar mutum da tursasawar canza addini.

Sai dai lamarin ya sha bambam da yadda Kotun ta ayyana domin kuwa ita budurwar da kanta ta bayyana cewar matashin ba sace ta yayi ba, bai kuma tursasamata canza addini ba har ma tace ta bishi jihar Kano bisa rajin kanta.

Tin dai a shekarar 2015, matashiyar mai suna Ese Oruru ta yi tattaki har zuwa jihar Kano wajen matashi Yunusa Dahiru domin su yi aure, lamarin da ya sanya matashin ya mika al’amarin zuwa ga fadar mai martaba Sarkin Kano na 14 na zuriyar Fulani, Mallam Muhammadu Sunusi II.

A shekarar 2016, jami’an ‘yan sanda suka samu matashiyar a jihar Kano, suka kuma mai da ita gaban iyayenta tare da tafiya da matashin zuwa can jihar Bayelsa.

A can jihar sun zargi matashi da laifin sace matashiyar tare da tursasa mata canza addini daga Kiristanci zuwa Musulunci.

Sai dai matashiyar, Ese ta karyata zargin da ake yi wa matashin na yin garkuwa da ita, ta ayyana cewar ta bishi jihar Kano ne bisa rajin kanta kuma ba canza addininta zuwa Musulunci ba tare da an tursasata ko an bukacin tayi hakan ba.

Tin dai a wannan lokacin al’umma da dama suka rika kira ga mutanen yankin arewacin Najeriya domin ceto rayuwar matashin, lamarin da ya wasu lauyoyi sukayi yunkuri nemo wa matashin adalci.

Sai dai zuwa yanzu, hakarsu ta gama cimma ruwa bayan hukuncin da kotun ta yanke.

Karin Labarai

UA-131299779-2