Akwai yiwuwar Fir’auna da mutanenshi sun iya Hausa – Bincike

dakikun karantawa

Muhammad Aliyu Dangalan

Masana tarihi sun bayyana yaren Hausa a matsayin yaren da Misiriwan zamanin Fir’auna suka yi amfani dashi wanda suka tabbatar da yiwuwar jin yaren a wajen Sarki Fir’auna.

Bayan wani rahoto da sashin Hausa na rediyon DW ya fitar akan batun, rediyon ta tattauna da wani masanin tarihi dan kasar Nijar wanda ya tabbatar da ikirarin kasancewar yaren Hausa a matsayin yaren da mutanen zamanin Fir’auna suke yi.

Masanin tarihi, Sule Garba, ya kara da cewa mutanen zamanin Fir’auna sun fara rayuwarsu ne a kauyen ‘Dan Baki’ dake garin Damagaram na Jamhuriyar Nijar.

Hakan na zuwa ne bayan da aka gano wani ginin tubalin ‘Pyramid’ irin na kasar Misra, ginin da turawa, masana tarihi suka tabbatar da Misirawan da sukayi kaura zuwa kasar Misira ne suka ginashi. Kuma shine ginin ‘Pyramid na farko kafin su gina na kasar Misra.

Haka zalika ya tabbatar da cewa yaren da Misirawan zamanin Fira’auna sukeyi mai suna Hieroglyphs, Hausa ce ba wani abu ba. Domin babu wani yare da ake rubuta “RAna” da ma’anar Rana (Sun) take fitowa idan ba yaren Hausa ba.

DABO FM ta gudanar da binciken cewa an fara tabbatar da alakar Hausawa da Misirawan zamamin Fir’auna shekaru 200-300 da suka gabata.

A shekarar 1938, fitaccen marubuci Werner Vicychl, ya tabbatar da alaka a cikin wani littafi da ya wallafa.

Hukumar kyautata ilimi da kimiya da al’adu ta majalisar dinkin duniya ‘UNESCO’ ta tabbatar da alakar yaren Hausa da yaren Misirawan zamanin Fir’auna a wani littafi mai suna ‘The peopling of ancient Egypt and the deciphering of Meroitic script‘.

Binciken DABO FM ya kara lulubo wasu kalmomi da suke kara tabbatar da Hausa a matsayin Misirawan zamanin Fir’auna;

An gano daga cikin fassara da akayi a yaren Misirawan lokacin, Misirawa suna kiran Fir’auna da sunan kalmar ‘Saraki’ wanda har ila yau yana amfani da ita a kasar Hausa wajen kiran Sarki.

A cikin kalmomin yaren Fir’aunawa akwai ‘Tuta’ – wacce take da ma’ana daya da ta yaren Hausa da kalmar ‘Qasa’ da nufin Ƙasa da sauren dubban kalmomi.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog