Anyi sabon gyara – 22/03/2020.
Faifan bidiyon ziyarar da shugaban kasar China, Xi Jinping , ya kai zuwa wani masallaci a kasar da ake yadawa a kafafen sada zumunta cewar shugaban ya kai ziyara domin neman addu’ar Musulmi ba gaskiya bane.
DABO FM ta tattara cewar ana yada bidiyon da cewar shugaban ya ziyarci masallacin domin neman addu’a bisa barkewar cutar ‘Coronavirus’ da ta hallaka daruruwan mutane a kasar.
Al’amarin da har ya kai ga wani babban malamin Najeriya yake amfani da labarin na bogi wajen kafa hujja akan rashin yarda da yace yayi da cutar ‘Corona Virus’ inda ya kirata da shirin Yahudawa.
Idan har malamin bai yarda da ita ba, ta yaya zai yadda cewa shugaban yaje wajen Musulmai neman addu’a domin samun yayewar cutar daga Ubangiji da suke bautawa?
DABO FM ta tabbatar da cewar babu tushe ko alamun gaskiya a maganar ziyarar shugaban domin kuwa shugaban yaje masallacin ne tin a shekarar 2016 a lokacin da yake rangadi arewacin kasar.
Bidiyon da gidan talabijin na kasar ya wallafa a shafinshi na Youtube wanda suka wallafa a ranar 20 ga watan Julin 2016.

Idan aka rubuta “Xi Jinping Mosque CCTV” za’a ga bidiyon da kwanan watan da aka wallafashi a tashar Youtube ko a sashin bincike na Google.
DABO FM tana kira ga al’umma musamman Musulmi cewar, sanin kai ne cewa karya da yada abu ba tare da bincike ba haramun ne kuma baya daga cikin kishin addini wajen yada karya domin farantawar rai ko jin dadinshi.
Daga bakin malaman Musulunci;
