//

Pantami ya fitar da sabbin tsarukan rijistar layin waya don inganta tsaro

0

Ministan sadarwa da tattalin arzikin na’ura, Dr Isah Ali Pantami, ya fitar da sabon tsarin rijistar layukan waya biyo bayan tabarbarewar harkokin tsaro a Najeriya.

A wata sanarwar mai dauke da sa hannun daya daga cikin mataimakan ministan, Dr Femi Adeluyi, ya fitar, ta bayyana sabbin tsarukan da za’a fara amfani dasu.

DABO FM ta tattara sabbin tsarukan kamar haka;

1. Katin dan kasa ne zai fara zama abinda za’a fara tambaya a yayin rijistar layi, wadanda ba yan Najeriya ba kuwa, zasu bayar da Fasfo da izinin shigowarsu Najeriya. Ministan ya bayar da wa’adi zuwa karshen shekara, kowane dan Najeriya ya bayar da katin dan kasa a shigar a cikin rijistarshi.

Masu Alaƙa  Pantami ya bada umarnin rufe layuka miliyan 9 da ake siyarwa ‘Masu Rijista’

2. A tabbatar da cewa amitattun dillalai ne zasu rika siyar da layi, haka zalika kamfani ne kadai zai iya yi wa layi rijista.

3. Layukan waya 3 kacal kowanne dan Najeriya zai iya mallaka.

4. A tabbatar da babu layin da zai yi aiki face sai da rijista.

5. A tabbatar da cewa kowa zai iya ganin bayanan da aka shigar wajen yin rijista kai tsaye ta waya.

6. Dole kamfanonin sadarwa su yaki ta’addanin ko barnar yanar gizo.

7. A tabbatar da rufe dukkanin wani ds aka samu da amfani wajen aikata miyagun laifuka.

Karin Labarai

Share.

About Author

Comments are closed.

%d bloggers like this:
©Dabo FM 2020